Hausa Fatwa podcast

Fatawowin Rahama: Q&A 11-15-2026

11/23/2026
0:00
53:07
Rewind 15 seconds
Fast Forward 15 seconds

Fatawowin Rahma


Rana: Lahadi, 5/6/1448 — 15/11/2026


Tambayoyi da Amsoshi tare da Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON


  1. ​ Shin mai bin mazhabar Malikiyya zai iya bin wata mazhaba, kamar mazhabar Hanafiyya ko Shafi’iyya, a kan batun haɗa salloli ko wasu mas’alolin addini?


  1. ​ Idan mutum ya yi wankan janaba, zai iya yin sallah da wannan wankan ko da bai yi alwala ba?


  1. ​ Shin ma’auratan da suka rabu ta hanyar khul’i za su iya sake auren juna?


  1. ​ Idan aka haɗa salloli, ta yaya mutum zai yi azkar ɗin bayan sallah?


  1. ​ Ya hukuncin wanda ya yi alwala, sannan yana cikin sallah sai ya ji ɗan fitsari yana fita?


  1. ​ Idan mutum yana wanka sai wani abu kamar fitsari ya fito, shin hakan yana ɓata wankan?


  1. ​ Yaya hukuncin yin Sallah kafin lokacin sallar farilla ya shiga?


  1. ​ Idan mutum ya tashi yin sallah a lokacin kiran sallar farko, shin sallar za ta kasance ƙiyamul-laili, ko kuwa lokacin ƙiyamul-laili ya riga ya wuce?


  1. ​ Mene ne hukuncin wanda yaci wasu kuɗi a makarantar da yake aiki, daga baya kuma ya tuba ya mayar da fiye da abin da ya ɗauka?


  1. ​ Shin malamin jami’a zai iya sauya jadawalin koyarwarsa?


  1. ​ Shin namiji zai iya yi wa macen da ba muharramarsa ba sallama?


  1. ​ Waɗanne abubuwa biyar ne da aka ambata a cikin hadithin da yake cewa “Idan aka jarrabe ku da su…”?


  1. ​ Yaya ingancin wannan addu’a? اللهم انت أمرتنا بدعاءك و وعدتنا بإجابتك…..zuwa karshe


  1. ​ Shin mace zata iya buɗe shagon siyar da kayan mata, sannan ta riƙa siyar da kayan da kanta?


  1. ​ Yaya hukuncin dillalin da ya ƙara farashi a kan kuɗin da mai kaya ya ce ya siyar?

More episodes from "Hausa Fatwa"